1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jordan ta gargadi Trump kan birnin Kudus

Yusuf Bala Nayaya
December 4, 2017

Kasar Jordan ta yi gargadi ga Shugaba Donald Trump na Amirka kan cewa a tsammaci babban tashin hankali muddin Amirka ta amince da birnin Kudus a matsayin babban birnin Isra'ila.

https://p.dw.com/p/2ohjv
USA Israel | Benjamin Netanjahu bei Donald Trump in Washington
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Ministan harkokin wajen Jordan Ayman Safadi ya fada wa sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ta shafin Twitter cewa wannan yunkuri zai sanya a samu tashin hankali a fadin kasashen Larabawa, ya kuma yi kafar ungulu ga kokari na samar da zaman lafiya a yankin.

A ranar Lahadi ne dai aka ji mashawarcin shugaban kuma sirikinsa Jared Kushner na fadin cewa shugaban na sake nazarin wannan matsaya ta birnin Kudus.

Rahotanni dai na nuni da cewa nan da ranar Laraba za a ji matsayar ta Trump kan birnin na Kudus ko zai tsaya a babban birnin Isra'ila, lamarin da zai sauya tsarin Amirka da shugabanninta  na Republican ko Democrats a gwamman shekaru.