1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jordan za ta cika muradin mayakan IS

January 28, 2015

Kasar ta ce a shirye take ta saki matar nan 'yar Iraki da ake tsare da ita saboda sa hannunta a harin kunar bakin wake a 2005 a birnin Amman idan har za a sako matukin jirginsu.

https://p.dw.com/p/1ES6O
Muath al-Kasaesbeh: matukin jirgin yakin Jordan
Muath al-Kasaesbeh: matukin jirgin yakin JordanHoto: picture-alliance/dpa

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Mohammad al-Momani, ya bayyana cewa kasar Jordan a shirye ta ke ta saki Sajida al-Rishawi idan har mayakan na IS za su sako Muath al-Kasaesbeh. Mohammad al-Momani ya bayyana hakane a wani jawabi da ya gabatar ta kafatr talabijin na kasar.

Sai dai bai yi wani karin bayani ba a dangane da Kenji Goto dan asalin kasar Japan wanda shi ma a yanzu haka ke hannun na kungiyar ta IS wanda ya bayyana a fefen bidiyo cewa mayaknan na IS sun bawa mahukuntan kasar ta Jordon sa'oi 24 su sako 'yar tawayen ta Iraki ko su halaka wannan matukin jirgi.

Daruruwan mutane ciki kuwa har da iyalan da wannan matukin jirgin sama ya fito sun tattaru a ofishin Firaminista a yammacin jiya Talata inda suke bukatar mahukuntran kasar su cika umarnin mayakan na IS wajen sakin al-Rishawi.

Mawallafi:Yusuf Bala
Edita: Umaru Aliyu