Angola na jimamin mutuwar Dos Santos
July 8, 2022Talla
A wata sanarwar da gwamnatin ta fitar a shafinta na Facebook, ta ce, tsohon shugaban kasar Jose Eduardo dos Santos, ya mutu ne a wani asibiti da ke birnin Barcelona na kasar Spain, bayan da ya sha fama da doguwar jinya. Za a kwashi akalla kwanaki biyar ana zaman makoki bayan da aka sassauta tutar kasar don girmama marigayin bisa umarnin Shugaba Joao Lourenco.
Ana tuna dos Santos da zama adalin shugaba da ya gudanar da shugabancincinsa na kusan shekaru arba'in a lokacin da Angola ta ke cikin hali na rashin tabbas, bayan da ta samu 'yanci kai daga kasar Portugal da ta yi mata mulkin mallaka.