José Eduardo dos Santos: Shugaban Angola mutu ka raba
Tun lokacin samun 'yancin kai har ya zuwa yanzu, a Angola shugaba daya ne ke yin mulki. Tun a shekara ta 1979 José Eduardo dos Santos ke yin mulki. Sai dai ya ce ba zai yi takara ba a zaben shekara ta 2017.
Injiniya na hako man fetir
Yana da shekaru 19 José Eduardo dos Santos ya shiga MPLA. Kungiya mai ra'ayin Makisanci da ta yi fafutukar samar da 'yancin kai na Angola daga Potugal. A 1963 ya samu zuwa Baku, da ke kasar Rasha a wancan lokaci, domin yin karatun aikin hako man fetir da kuma sadarwa, kafin ya shiga harkokin soji. A 1970 ya koma gida Angola.
Ministan harkokin waje a karkashin gwamnatin Neto
Bayan samun 'yanci kai na Angola daga Potugal, a 1975 yakin basassa ya barke tsakanin kungiyoyin da suka yi fafutukar samun 'yanci na MPLA da UNITA da kuma FNLA. Babban birnin kasar wato Luanda, ya kasance a karkashin ikon MPLA. Agostinho Neto wanda hoton sa ke a kai shi ne shugaban kasa na farko kana kuma ya kafa tsarin mulkin jam'iyya daya. José Eduardo ya rike ministan fasali a yayin mulkinsa.
Kawance da Rasha wadda a wacan loakaci ake kira USSR
A cikin watan Satumba na 1979 Neito ya mutu a Moscow. Bayan kwanaki goma MPLA ta zabi José Eduardo ya zama sabon shugaban kasa. Ya kara karfafa hulda da kasashe masu bin ra'ayin tsarin kwamunisanci kamar su Rasha da Kyuba da Jamus ta Gabas. A 1981 José Eduardo ya kai ziyara Jamus ta Gabas, a nan hoton sa ne tare da babban sakataran kwamitin zartaswa na SED, Erich Honecker na Jamus ta Gabas.
Duniya da mabanbanta ra'ayi: Yamma na kalubalantar gabas
A lokacin ziyarar sa a Jamus a 1981 José Eduardo dos SantoS ya ziyarci kofar Brandenburg da kuma katangar Berlin. Wadannan abubuwa guda biyu misalai ne na yakin cacar baka tsakanin kasashen yammaci da na gabashin. Angola ma dai ta kasance a tsakiyar irin wannan yaki, inda ta ke samun goyon bayan kasashen gabashi a yakin da ta yi da UNITA, inda su kuma Amirka da Afirka ta Kudu ke goyon bayan UNITA.
Kafada da kafada tare da Kyuba
Gwamnatin Kyuba ma ta bai wa MPLA taimakon sojoji. Kimanin sojojin Kyuba dubu 40 ne suka kasance a Angola, misali a 1988 a Cuito Canavale. Yakin da ya kasance mafi muhimmanci. Kafin bayan shekaru uku a cimma yarjejeniyar zaman lafiya ta farko a Potugal.
An ci gaba da yaki duk da cimma yarjejeniya
Bayan rinjayen da MPLA ta samu a majalisa a zaben 1992, sai dai José Eduardo dos Santos bai samu rinjaye na bai daya a zaben ba, UNITA ta ci gaba da yin yaki domin ta ce an tafka magudi.
Kasashen yammacin duniya sun daina shiga yakin Angola
Bayan yakin cacar-baka, kasashen yammacin duniya sun dakatar da shiga yakin Angola. A 1993 Amirka ta amince da gwamnatin MPLA saboda ta soma zama ta 'yan jari hujja. Bayan kawo karshen wariyar launin fata UNITA ta daina samun taimakon Afirka ta Kudu. A 1994 aka cimma yarjejeniar zaman lafiya, amma ba tare da cimma nasara ba, José Eduardo dos Santos ya yi amfani da karfin soji.
Hulda da Kabila na Kwango
A yakin Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango a 1988 Laurent-Désiré Kabila wanda hoton sa ke a sama ya rika samun taimakon Angola. Inda wasu daga cikin mayakan UNITA da suka balle suka koma. Angola ta zama kasa mafi karfin sojoji a yankin gabashin Afirka.
An samu nasara a kan Savimbi
Takunkumin haramta sayar da makamai a kan UNITA ya rage ma ta karfi, kana kasashen duniya sun ware ta. A ranar 22 ga watan Fabarairun, 2002 aka kashe jagoran UNITA Jonas Savimbi wanda hoton sa ke a sama. A wannan shekara UNITA da MPLA suka cimma yarjejeniyar zaman lafiya. Yakin dai shi ne mafi muni a Afirka, inda ya lakume rayukan mutane miliyan guda kana wasu miliyan 40 suka yi hijira.
Abin da ya saura na yakin
Shekaru da dama bayan yakin na Angola, ana iya ganin irin mummunar barnar da ya haddasa. Kamar a wannan hoton da aka yi misali da shi a shekara ta 2009. Kuma a Cabinda da ke arewacin kasar, har yanzu ana ci gaba da samun tashin hankali tsakanin kungiyoyin 'yan aware na FLEC.
An dage zabubbuka ko an soke
Bayan zaben 'yan majalisun dokoki da aka gudanar a shekara ta 1997 wanda MPLA ta samu gaggarumar nasara da kaso 81 cikin 100 yayin da UNITA ta samu sama da kaso 10 kacal, an yi ta zargi na tafka magudin zabe. A karshe dai a shekara ta 2009 an soke zabubbukan da aka shirya gudanarwa. José Eduardo dos Santos ya ci gaba da kasancewa a kan mulki.
Hulda mai tsauri
A shekara ta 2011 shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ziyarci Angola. Sai dai abubuwa na raya kasa kalilan ne Jamus ta yi a Angola. Hulda tsakanin kasashen biyu na da tsauri. Kanfanonin Jamus kalilan ne ke saka jari a kasar ta Angola.
Haramta 'yan adawa
A wani abu tamkar koyi da juyin-juya hali a kasashen Larabawa, a shekara ta 2011 masu adawa da gwamnatin José Eduardo dos Santos sun yi ta zanga-zanga. Sai dai 'yan sanda sun rika murkushe su. Wadanda aka kama an kule su a gidajajen yari. A shekara ta 2013 masu gadin fadar shugaban kasa sun harbe 'yan adawa biyu har lahira. Kungiyoyin kare hakin dan Adam na zargin 'yan sanda da take hakin jama'a.
A karshe ya lashe zabe ta wata hanya daban
A shekara ta 2010 majalisar dokoki ta yi kwaskwarima ga dokokin zabe tare da soke zaben shugaban kasa. A zaben shekara ta 2012 MPLA ce ta samu rinjaye da kaso 71 cikin 100. Bayan shekaru 32, a karon farko José Eduardo dos Santos ya samu gindin zama da sunan demokaradiyya.
Tare da mai dakinsa
Bayan harkokin sa na soji José Eduardo dos Santos ya kan kula da iyalan sa. Ya yi aure sau da yawa, amma matar sa ta yanzu ita ce Paula dos Santos wadda hoton ta ke sama. Ya hadu da ita a lokacin da take aikin kula da fasinjoji a cikin jirgin sama. Sun yi aure a 1991 suna da 'ya'ya hudu. A zaben shekara ta 2017 da ke tafe Paula dos Santos za ta tsaya takarar 'yar majalisa a karkashin tutar MPLA.
'Yar José Eduardo dos Santos Isabel ita ce mace mafi arziki a Afirka
'Yar José Eduardo dos Santos ta farko wadda ya samu da wata 'yar kasar Rasha Tatiana Kukanova ta mallaki kanfanonin sadarwa na wayar tafi da gidanka na Unitel a Angola. Matar sa ta biyu kuma ita ce Filomena de Sousa da ya aura a lokacin da yake rike da matsayin ministan harkokin waje.
Hulda da China
China sabuwar abokiyar hulda ta Angola. Kasar ce kan gaba wajen sayan man fetir na Angola kana ta kan yafe ma ta kudaden rance. Sannan kanfanonin China na yin gine-gine don kara inganta biranen kasar, misali wannan hoto da ke sama na unguwar Kilamba da ke a Luanda. Sabannin hukmar IMF, China ba ta neman bayanai game da yadda ake kare hakin dan Adam a kasar gabanin ba da rance.
Arziki da talauci
Bayan arzikin man fetir na miliyoyin daloli da kasar ta ke samu, 'yan Angola da dama na fama da talauci. Kasar na da adadi mafi girma na yara kanana da ke mutuwa a duniya. A tsakiyar birnin Luanda, akwai wurare da dama da ba a kwashe ruwan datti. Asibotocin da ke akwai sun fi karfin talaka saboda tsada. Kuma babu cikakken ilimi ga 'yan makaranta.
Mutumin da ba ya bayyana kansa
José Eduardo dos Santos bai cika bayyana kan sa a bainar jama'a ba. Misali bai cika yin hira da 'yan jarida ba, haka ma bai cika yin jawabai ba. A shekarun baya-bayan nan José Eduardo dos Santos ya na yawan tafiye-tafiye zuwa Spain domin a duba lafiyar sa. Bayan shugaban Equatorial Guinea Teodoro Obiang shi ne shugaba mafi dadewa a kan karagar mulki a Afirka da kwashe shekaru 37 yana shugabanci.
Bayyana magajinsa
Bayan dos Santos ya sanar da cewar ba zai tsaya takara ba a zaben watan Agusta na shekara ta 2017, MPLA ta zabi ministan tsaro João Lourenço da ya yi takara a zaben 'yan majalisu, wanda shi ne ake tsammani zai gaji José Eduardo dos Santos inda shi kuma zai ci gaba da kasancewa jagoran jam'iyyar MPLA, da ake ganin zai rika taka rawa wajen tafiyar da harkokin mulki a Angola.