JTF ta ce Abubakar Shekau ya mutu.
August 20, 2013Talla
Abubakar Shekau ya mutu ne a cewar JTF a sakamakon raunikan da ya samu a wani gumurzun da ƙungiyar ta sha da dakarun ƙungiyar ta Boko Haram a ƙarshen watan Yuni da ya gabata.
Sanarwa da rudunar ta bayar ta ce an kai Shekau ɗin a ƙasar Kamaru domin yin jinya amma ya mutu tsakanin ranar 25 ga watan Yuni zuwa uku ga wannan wata Augusta. Har yazuwa yanzu dai ba da tabbas dangane da mutuwar ta jagoran na ƙungiyar ta Boko Haram.
Mallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu.