1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juba: Kasashe na rufe ofishin jakadancinsu

Abdul-raheem HassanJuly 11, 2016

Magoya bayan Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar na ci gaba da lugujen wuta a babbar birnin kasar Juba.

https://p.dw.com/p/1JN4t
Südsudan Juba SPLA Rebellen
Hoto: Getty Images/AFP/S. Bol

Dakarun da ke goyon bayan shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir da mataimakinsa Riek Machar na ci gaba da luguden wuta a wannan Litinin. Rahotanni da ke fitowa daga babbar birnin kasar Juba na cewa ana ci gaba da jin karar fashewewar bama-bamai . Wannan dai shi ne rana ta biyar tun barkewar rikicin a ranar Juma'ar da ta gabata a lokacin da shugabannin ke shirin tattauna shirya bukuwar cikar kasar shekaru biyar da samun 'yancin kai.

Kawo yanzu dai rahotanni na cewa an samu asarar rayukan mutane dari biyu daga ranar Juma'a zuwa yau. Wannan na faruwa ne sa'o'i kadan bayan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi kira ga dukkanin bangarori da ke fada da juna da su kawo karshen tashin-tashina da ke sa 'yan kasar zama a kan kafafunsu. Hukumomin agajin gaggawa da ofisohin jakadancin kasashen waje na rufewa.