1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka na shirin daukar mataki kan Saudiyya

Mahmud Yaya Azare AH
March 1, 2021

Masu rajin kare hakkin bil adama na kasa da kasa, sun bukaci shugaban Amurka Joe Biden, da ya dau matakin ba sani ba sabo kan yarima mai jiran gado na Saudiyya,biyo bayan tabbatar da ba da umarnin kisan Khashoggi.

https://p.dw.com/p/3q4IK
Kombobild Joe Biden, US-Präsident & Salman ibn Abd al-Aziz, König Saudi-Arabien
Joe Biden tare da sarkin Saudiyya Salman ibn Abd al-Aziz,

A ranar Juma’a ne dai Amirkan ta wallafa sakamakon wani rahoton sirri da hukumar leken asirinta, CIA ta tattara, wanda ya tabbatar da cewa, Bin Salman ya amince da kamo Jamal Khashoggi ko kuma kashe shi, a birnin Santambul na Turkiyya a Oktoban shekarar 2018, inda bayan kashe shi aka yi gunduwa-gunduwa da gawarsa. Kamar yadda rahoton ya kara tabbatar da cewa, jirage biyu daga cikin jiragen da jami’an tsaron Saudiyya suka yi amfani da su zuwa Turkiyya domin kashe Jamal Khashoggi, mallakin Muhammad Bin Salman ne. Tuni dai ma’aikatar lura da baitulmalin Amirka ta sanar da matakin kwace kadarorin wasu daga cikin na hannun daman  Yarima Bin Salman tare da sanya su cikin bakin kundinta, sai dai ba ta ce komai ba dangane da daukar mataki kan Yariman na Saudiya da t ce shini kanwa uwar gami a kisan gillar da ya jijjjiga duniya.

Amirka na shirin daukar mataki kan Saudiyya kan kisan Kashogghi 

US und Saudi Flaggen
Hoto: MATTHEW CAVANAUGH/Epa/dpa/picture-alliance

Turkiya, inda aka yi wannan aika-aikar a kasarta,da kuma matar da Khashoggi ke shirin aura, Khadijah Jinkeez, suka ce, sun zura ido suna jira su ga irin hukuncin da gwamnatin Biden din za ta dauka kan Yarima Bin Salman din. Duk da cewa a halin yanzu, Saudiya tayi fatali da rahoton, sai wasu masharhanta na hasashen cewa, mai yiwa akwai wani abu a kasa da zai iya faruwa, musammun ma jita-jitar tsige Bin Salman din daga matsayinsa na Yarima mai jiran gado, kasancewar tun kafin ba da da wannan rahoton,Biden din ya sha alwashin cewa, ba zai taba yin ta,amuli karkashin gwamnatinsa da Yarima Bin Salman ba.