1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasashen duniya sun soki lamirin Netanyahu

Abdoulaye Mamane Amadou
September 11, 2019

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi Isra'ila da ta guji duk wani abin da zai iya yin karan tsaye game da batun sake komawa kan teburin sulhu domin samun zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinawa.

https://p.dw.com/p/3PNpw
Ministerpräsident Netanjahu zur Annektion des Jordantals
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/O. Balilty

Stefan Dujarik Kakakin sakataren Majalisar Dinkin Duniya ne ya bayyana haka a yayin wata ganawa da manema labarai, inda ya yi kakkausar suka ga matakin da Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ke shirin dauka idan ya lashe zabe, na mamaye kwarin gabar kogin Jodan tare da mayar da shi mallakar Isra'ila.

Ita ma dai kasar Saudiyya ta bayyana matakin a matsayin wani mai hadari, tana mai fatali da kudrin tare da bayyana shi a matsayin wani yukuri da ya sabawa taswirar Majalisar Dinkin Duniya, tare da kira da a gudanar da taron gaggawa na kasashe manbobin kungiyar kasashen musulmai ta duniya OIC, a yayin da a ita kuwa Turkiya ta kira kalaman da cewa irin na wariyar jinsi ne.

A yayin kaddamar da yakin neman zabensa ne Firaministan na Isra'ila ya baiyana anniyar mamaye wani bangaren na Jodan tare da shigar da shi cikin Israila.