Kalubale a zagaye na farko na zaben Uganda
February 19, 2016Talla
An kama Madugun 'yan adawar kasar ta Uganda ne na wani dan lokaci, bayan a jiya Alhamis bayan da ya gano inda magoya bayan shugaban mai barin gado ke aringizon kuri'a a wani gida a birnin Kampala. Zaben dai ya gamu da tarin matsaloli da suka hada da babban tsaiko da aka samu kafin soma zaben, da toshe kafofin sadarwa na zamani, abun da ya haifar da bacin ran masu zabe da ma masu sa ido na kasashen waje.
Tuni dai kasar Amirka ta yi Allah wadai da kamun da aka yi wa madugun 'yan adawar, inda ta ce hakan ya sabama matakkin da kasar ta Uganda ta dauka na shirya zaben cikin haske amma ake yi wa 'yan adawa furjin mussa.