1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin ya damu da kame jami'insa da Italiya ta yi

Binta Aliyu Zurmi
September 5, 2019

Shugaba Putin na kasar Rasha, ya bayyana damuwa danagne da kame wasu jami'in kasarsa da hukumomin Italiya suka yi bayan zarginsu da leken asiri.

https://p.dw.com/p/3P8ZN
Russland | 5. Eastern Economic Forum 2019 - Vladimir Putin während Treffen mit Hu Chunhua
Hoto: picture-alliance/Russian Look

Shugaban na Rasha ya kuma ce Italiyar ta yi hakan ne bisa umurnin Amirka, abin kuma da ya ce zai bata dangantakarsu da Washington.

A ranar 30 ga watan jiya ne dai mahukuntan Italiya, suka kama Alexander Korshunov, babban darakta a ma'aikatar da ke kera injunan jiragen yaki a filin jirage na birnin Naples.

Sai dai ma'aikatar kula da harkokin cikin gidan Italiya, ta ce bata da abin da za ta ce kan wannan batun.

Shugaba Putin ya ce kama jami'in na kama da wata gasa marar ma'ana da Amirka ke kokarin yi da Rasha.