1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kamaru: Matsalar ilimi ga yara wadanni

August 22, 2017

Akalla kashi 80 cikin 100 na yara wadanni 'yan kabilar Baka mazauna kauyen Lomie da ke a gabashin kasar Kamaru ba sa zuwa makaranta saboda kuncin rayuwa da yankin ke ciki.

https://p.dw.com/p/2ielE
Kamerun Flüchtlingslager Minawao
Hoto: AFP/Getty Images/R. Kaze

Bincike ya gano cewa galibin yaran na shiga cikin wasu ayyukan kwadago saboda walau taimaka wa iyayensu, ko kuma neman warware wasu mastalolinsu na kansu. A wata makarantar firamare ta gwamnati da ke Payo da ke arewa maso yammacin Lomie makarantun yankin na dauke da yara wadanni 'yan kabilar Baka akalla 300 amman fiye da rabinsu ba sa zuwa makaranta don kuwa galibinsu na bin iyayensu zuwa gonaki ko kuma aikin sare-saren itatuwan katako da wasu kamfanonin kasashen ketare ke yi a yankin.

'Yan kabilar ta Baka suna zama ne a wani yanki na tsawon lokaci amman a cikin shekaru 20 da suka wuce kamfanonin daga wasu kasashen Turai da na China sun shigo yankin. Kamfanonin na daukar yaran wadanni don yi masu aiki inda ake biyunsu kudin da bai taka kara ya karya ba amman dole yaran ke karba saboda halin talauci da suka sami kai a ciki. A kokarin kawo wa wadannan yara dauki kungiyoyi kare hakkin jama'a ciki har da asusun kula da yara na UNICEF suka zabura don karfafawa yaran gwiwa kan komawa makaranta inda a kullum suke bi gida-gida suna daukar yaran da basu bi iyayensu ba don kai su makaranta.

Wani basaraken gargajiya a kauyen Aleka Raymond ya bayyana takaici kan rashin taimakon raya yankin daga kamfanonin da ke cin moriyar ayyukan da suka yi a wajen, musamman na samar masu ko da makaranta ya ce kana iya ganin makarantun da aka yi watsi da su. Na sani da a ce suna gine da kyau da kayan koyarwa da yara za su yi sha'awar karatu. Halin yanzu dai an sami yara Wadanni da suka bayyana sha'awar zuwa makaranta don samun ilimin zamani.