1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gwamnati Zimbabuwe tana kama 'yan adawa

Yusuf Bala Nayaya SB
August 8, 2018

Bayan zaben Shugaba Emmerson Mnangagwa na Zimbabuwe an fara kame-kamen 'yan adawa da ake gani kamar yadda ya faru bayan zaben 2008 lokacin tsohon Shugaba Robert Mugabe. Matakin da 'yan fafutika ke adawa shi.

https://p.dw.com/p/32p8x
Simbabwe Tendai Biti, Oppositioneller & ehemaliger Finanzminister
Hoto: Getty Images/AFP/J. Njikizana

Bayan da aka kammala da zabe a kasar Zimbabuwe da dama na ganin shike nan komai ya tafi daidai, saura da me abubuwan da ke biyo bayan zaben na Emmerson Mnagagawa na zama abubuwa da ke tada hankali na al'umma da ma 'yan fafutika.

Letwin Mugabe uwa ce ga yara biyu 'yar shekaru 38 kuma, ta bayyana cewa bakin tashi ta yi daga bacci bayan da ta bude ido ta ga wasu jami'an tsaro a gidanta da sunan sun zo neman wani madugun adawa da ya taba zama a gidan, sun dai maguza mijinta da wasu makota lokacin neman bayani kan dan adawa.

Simbabwe Präsidentschaftswahl Inhaftierung Oppositioneller
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Wannan daya ne daga cikin misalai na halin da 'yan adawa bisa jagorancin  Nelson Chamisa ke fuskanta inda jami'an tsaro ke masu dauki daidai. Kungiyar Human Rights Watch  ta ce ta tattara bayanai na take hakkin bil Adama a wannan kasa.

Zaben shekarar ta 2018 ana kallonsa a matsayin wanda aka yi shi cikin kwanciyar hankali a Zimbabuwe amma kisan da jami'an tsaro suka yi wa 'yan adawa shida a ranar Laraba a birnin Harare baya ga kame-kamen wasu da dama wannan ya sauya kallon da ake wa zaben.

Simbabwe Wahlen
Hoto: Getty Images/AFP/M. Longari

Zimbabuwe dai ta samu kanta da tunanin samun sabuwar gwamnati tun bayan kawar da Robert Mugabe a watan Nuwamba na 2017. Fata da al'umma ke da shi dai bai wace samun ci-gaba ba sabanin komawa cikin yanayi na take hakkin bil Adama kamar yadda aka gani shekarun baya. Sai gashi rahotanni na nuni da cewa tsohon ministan kudi kuma jagoran adawa Tendai Biti ya fada komar 'yan sanda a lokacin da yake kokarin tsallaka iyaka don neman mafakar siyasa a Zambiya kamar yadda lauyansa ya bayyana. Hakan dai na zuwa bayan da gwamnatin Zimbabuwe ta ce tana nemansa bisa zargin tada rikici da ya biyo bayan zabe.