Kame-kamen 'yan fafutika a China
March 25, 2016Kungiyar Amnesty International ta yi kakkausar suka ga mahukuntan China a ranar Juma'ar nan, bayan da wani dan jarida dan asalin kasar da ke zaune a birnin New York na Amirka ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa iyayensa da dan uwansa sun bace.
Kamen na iyalan Wen Yunchao na zama na baya-bayan nan cikin kame-kame da mahukuntan na China ke yi tun bayan da aka fitar da wata budaddiyar wasika da ke kira da shugaba Xi Jinping ya sauka daga mukaminsa.
Wen Yunchao wanda ke zama fitacce cikin masu sukar mahukuntan wannan kasa ta China da ke zaune a New York, ya ce wani daga cikin 'yan uwansa ya fada masa cewa iyalan nasu uku wasu jami'an gwamnati sun yi gaba da su daga gidansu da ke lardin Guangdong ba tare da wani jawabi ba. A cewar William Nee, dan China da ke bincike a kungiyar Amnesty International kamata ya yi gwamnati ta daina kame-kame na bai gaira saboda zargin waccen budaddiyar wasika.