Kamfanoni da dama sun janye daga taron Saudiyya
October 19, 2018Manyan kamfanonin kasuwanci na manyan kasashen duniya na kara janyewa daga taron kasuwanci da kasar Saudiyya ta tsara a mako mai zuwa, abin da ke kara nuna rikita-rikitar siyasa da kasar ta samu kanta yayin da take neman hanyoyin bunkasa tattalin arziki domin kauce wa dogaro da man fetur.
Kamfanonin sun dauki matakin sakamakon bacewar dan jarida Jamal Khashoggi wanda ake zargi an kashe shi a kofishin jakandancin Saudiyya da ke birnin Santambul na Turkiyya, kuma yanzu haka mahukuntan Turkiyya suna bincike inda suka ce sun gano wajen da aka kashe dan jarida kafin yanka shi gunduwa-gunduwa.
Shugaba Donald Trump na Amirka ya ce yana tunain lallai an kashe dan jaridan Jamal Khashoggi amma yana jiran bincike duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci sakamakon abin da ya aikata.