An shawarci shugabanni game da sauyin yanayi
September 27, 2019Talla
Matashiyar 'yar fafutukar kare muhalli Greta Thunberg ta bi sahun dubban al'ummar da zasu gadanar da rangadin a yankin Arewa Amirka don neman gwamnatocin kasashen duniya su dauki matakin gaggawa a harkokin sauyin yanayi. A na sa ran dubban jama'a za su fito a dama da su daga birane 80 na kasar Kanada tun daga wannan rana ta Juma'a.