Kanada za ta shiga yakin da ake da 'yan IS
October 3, 2014Talla
Firaministan Kanada Stephen Harper ne ya ambata hakan a wannan Juma'ar inda ya ke cewar sojinsu za su shiga a dama da su a yakin ne na tsawon watanni shidda kacal kuma za su kai farmaki ne kawai ta sama.
To sai dai kafin Kanadar ta shiga wannan yaki sai majalisar dokokin kasar ta bada izinin yin hakan, batun da masu aiko da rahotanni ke cewar da wuya a samu matsala kasancewar jam'iyyar firaministan kasar ta masu ra'ayin 'yan mazan jiya ce ke da rinjaye a zauren majalisar.
Idan har majalisar ta amince da wannan bukata ta firaministan, to Kanada za ta zama kasa ta baya-bayan nan da za ta shiga gammayar kasashen da ke rufawa Amirka baya wajen kawo karshe aiyyukan 'yan IS din.