Kanada za ta tura soji da jirage zuwa Mali
March 19, 2018Ministan tsaron na Kanada ne Harjit Sajjan ya sanar da wannan labari a wannan Litinin din, inda ya ce sojojin na kasarsa za su je Mali ne da jirage masu saukar Ungulu sanfarin Chinook, domin daukan kayayakin aikin rundunar ta MINUSMA cikin gaggawa ya zuwa wasu yankuna a duk lokacin da bukatar hakan ta taso, sannan da jirage masu saukar ungulu sanfarin Griffon wadanda su kuma za su kasance na rakiyar sojoji domin basu kariya ta sama a cewar ministan.
Yayin wani taron manema labarai a birnin Ottawa, Ministan tsaron kasar ta Kanada tare da halartar ministar harkokin wajen kasar Chrystia Freeland, ya ce sojojin na Kanada da za a tura a yankin Arewacin kasar ta Mali sun hada da maza da mata, sai dai kuma ya ce sai bayan sun kare tattaunawa da Majalisar Dinkin Duniya kafin su sa rana. A baya dai Kanada ta ce tana iya aikewa da sojojinta har 200 zuwa kasar ta Mali.