1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karbe iko da yankunan da ke hannun 'yan tawayen Sudan ta Kudu

December 23, 2013

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta ce sojinta sun tashi haikan wajen fatattakar 'yan tawayen da biyayya ga tsohon shugaban kasar Riek Macher da suka kwace wasu yankunan kasar

https://p.dw.com/p/1AfBt
Shugaba Salva Kiir na Sudan ta KuduHoto: Reuters

Shugaban kasar Salva Kiir ne ya bayyana hakan a wannan Litinin din lokacin da ya ke jawabi ga majalisar dokokin kasar, inda ya kara da cewar sojinsu yanzu haka a shirye suke da su dannan garin Bor wanda ke hannun 'yan tawaye don maido da shi karkashin ikon gwamnati.

Shi ma dai kakakin rundunar sojin Sudan ta Kudun Philip Aguer ya ce mutanensu a shirye su ke da su shiga garin na Bor da jihar Unity inda 'yan tawayen yanzu haka ke iko da sun.

A dauara da wannan kuma, babban jami'in hukumar bada agaji ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kasar Toby Lanzer ya ce halin da jama'ar kasar ke ciki na cigaba da munana domin da dama daga cikinsu yanzu haka sun kauracewa matsugunansu inda suka shige dazuka domin tsira da rayukansu.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal