1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yarjejeniyar kare 'yan gudun hijira

Suleiman Babayo
December 17, 2018

Sabuwar yarjejeniyar kare 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta samu karbuwa daga kasashe kusan 170 na duniya.

https://p.dw.com/p/3AFqo
Rom - Demonstration gegen Einwanderungspolitik in Italien
Hoto: picture-alliance

Babban zauren mashawartar Majalisar Dinkin Duniya ya amince da yarjejeniya kan 'yan gudun hijira tsakanin kasashen duniya, mako guda bayan amincewa da irin wannan yarjejeniyar. Kusan kasashe 170 suka yi alkawarin taimakon mutanen da suke tserewa daga yaki da hukuba.

Fiye da mutane milyan 24 suke gudun hijira kimanin rabi suna kasa da shekaru 18 da haihuwa a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya. Kasashen duniya 10 suka karbi bakuncin kashi biyu bisa uku na daukacin 'yan gudun hijira.