1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Harin Gaza ya hallaka jami'an tsaro

Abdoulaye Mamane Amadou
August 28, 2019

Hukumomi a Zirin Gaza sun kara karfafa matakan tsaro jim kadan bayan tarwatsewar wasu abubuwa masu fashewa a kusa da shingen binciken ababen hawa na jami'an 'yan sanda, wanda ya yi sanadiyar mutuwar 'yan sandan

https://p.dw.com/p/3Obis
Gazastreifen Hamas Sicherheitskräfte
Hoto: AFP/Getty Images/M. Hams

Ma'aikatar cikin gidan yankin Falasdinawa ta bayyana cewa an kara karfafa matakan tsaron kan muhimman hanyoyi a yankin zirin Gaza, sakamakon kai harin da aka yi a wajen shingen jami'an tsaro.

A nata bangaren rundunar sojan Isra'ila da ta yi ruwan bama-bamai kan wasu wuraren da ke karkashin ikon kungiyar Hamas ta nesanta kanta da fashewar ababen, sai dai a share daya Isra'ilar ta rage yawan man fetur din da ta ke bai wa yankin na zirin Gaza a matsayin martani kan hare-haren rokoki da ta ce ta fuskanta daga yankin.