1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sasanta rikicin Jamus da Saudiyya

Suleiman Babayo ZMA
September 26, 2018

Kasashen Jamus da Saudiyya sun kawo karshen takaddamar diflomasiyya da ta janyo janye jakadan Saudiyya daga kasar Jamus.

https://p.dw.com/p/35Wzf
USA Deutschland und Saudi-Arabien legen diplomatische Krise am Rande der UN-Vollversammlung bei | Heiko Maas und Adel bin Ahmed Al-Jubeir
Hoto: imago/photothek/F. Gaertner

Kasashen Jamus da Saudiyya sun amince da kawo karshen takaddamar diflomasiyya da ta janyo kasar ta Saudiyya ta janye jakada a birnin Berlin na Jamus tare da hukunta kamfanonin Jamus da ke aiki a kasar.

Ana sa ran kowane lokaci daga yanzu Saudiyya za ta mayar da jakada a kasar Jamus. An samu takun saka tsakanin kasashen sakamakon kalaman tsohon ministan harkokin wajen Jamus Sigmar Gabriel kan manufofin Saudiyya a kasashen Gabas ta Tsakiya, musamman yakin da ke wakana a kasar Yemen.

Ministan harkokin waje na yanzu Heiko Maas ya kwashe lokaci yana neman hanyar warware rikicin tsakanin kasarsa ta Jamus da kua Saudiyya har zuwa wannan Talata da ya magance batun lokacin da ya tattauna da takwaransa na Saudiyya Adel al-Jubeir a taron shekara-shekara na MDD da ke gudana a birnin New York na Amirka.