1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karzai ya ki yin sulhu da 'yan Taliban

June 19, 2013

Shugaban Afghanistan Hamid Karzai ya ce matikar ba 'yan kasarsa ba ne za su jagorancin zaman tattauanawa da 'yan Taliban, to ba shi ba halartan sulhu a Doha na Qatar.

https://p.dw.com/p/18tCG
Hoto: Shah Marai/AFP/Getty Images

Gwamnatin Afghanistan bisa jagorancin Hamid karzai ta bayyana aniyarta ta kaurace wa taron sulhunta rikicin da ke tsakaninta da 'yan Taliban a Qatar matikar dai ba 'yan kasar ne za su jagorance shi ba. Fadar mulki ta Kabul ta yi wannan barazana bayan da ta samu tabbacin cewa gwamnatin Amirka za tattaunawa kai tsaye da masu kaifin kishin addinin a Doha inda suka bude reshensu; ta na mai cewa ya saba wa yarjejeniyar da ke tsakanisu.

Yayin da ya ke mayar da martani a Tarayyar Jamus inda ya ke ziyarar aiki, shugaba Amirka Barack Obama ya nunar da cewar wannan ita ce hanya mafi a'ala ta shawo kan 'yan Taliban domin su daina bude wuta. Yayin da ya ke magan da yawun kungiyar da ke da kaifin kishin addini Muhammad Sohail Shaheen ya bayyana wa tashar telebijin ta Aljazeera cewa ba ta da niyar tsagaita bude wuta a lokacin tattaunawar. Ko da a wannan larabar ma dai, sai da kungiyar taliban ta kai wani harin roka a sansanin sojojin sama da ke Bagram inda sojojin Amirka hudu suka mutu.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Zainab Mohammed Abubakar