Karzai yace ya gana da yan Taliban
April 6, 2007Shugaban lkasar afghanistan Hamid karzai yace ya gana da wasu yan kungiyar taliban a kokarinsa na sansanta rikicin kasar.
Karzai yace bayan ganawara komitin Taliban dana gwamanai,shi kansa ya gana da wakilan taliban amma banda Mullah Omar.
A wani labarin kuma wani dan kunar bakin wake ya kashe akalla mutane 5 a birnin kabul na kasar Afghansitan.
Yan sanda sunce mutumin yana zaune ne cikin motarsa a wajen majalisar dokokin kasar a lokacinda ya dana bam din yayinda wasu yan sanda suka nufi inda yake.
A kudancin kasar kuma,yan kungiyar Taliban sun kame lardin Khak Afghan,inda yan sanda suka janye a lokacinda yan taliban din suka kaiwa yankin hari.
Wannan kuwa ya faru ne a lokacinda yan sanda suke ci gaba da neman wasu maaikatan agaji 2 yan kasar Faransa da wasu yan kasar ta Afghanistan su 3 wadanda yan taliban sukayi garkuwa da su tun ranar talata.