1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasafin kudin Najeriya ya shiga rudani

February 20, 2024

A wani abin da ke zaman sabuwar barazana ga tarrayar Najeriya, kasafin kudin kasar na 2024 ya fada rudani sakamakon tashin farashin dalar da ke zaman ma'aunin kasafin.

https://p.dw.com/p/4cd3k
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin gabatar da kasafin kudi ga majalisa
Shugaban Najeriya Bola Tinubu yayin gabatar da kasafin kudi ga majalisaHoto: Ubale Musa/DW

Najeriyar dai ta yi kasafin Triliyan 28.7 ne bisa Naira 800 kan kowace dalar Amurka guda kafin hauhawar ta kai Dalar zuwa Naira 1600 da doriya a halin yanzu.

To sai dai kama daga kokarin biyan basuka ya zuwa kudaden aiyyukan tsaro da bukatun more rayuwa dai, shirin masu mulkin Abujar a shekarfar bana na neman rushewa yanzu haka.

Karin Bayani: Najeriya: Kasafin kudin Tinubu na farko

Shugaba Tinubu yayin gabatar da kasafin kudi a majalisa
Shugaba Tinubu yayin gabatar da kasafin kudi a majalisaHoto: Ubale Musa/DW

Abujar dai alal ga misali ta tsara biyan Naira Triliyan 8.25 da sunan uwar kudi dama bashi na kasashen waje, kafin rushewar da ke barazanar kai kasar zuwa gaza cika alkawarin da ke tsakaninta da yan bashin na waje ko kuma neman karin kaso dari cikin dari na kudaden a nan gaba.

Kuma ko bayan nan akwai tsoron tashi cikin farashin dala na iya shafar bukatun kasar na yakar rashin tsaro da ke neman karkata zuwa ga zamani da nuifn tunkarar matsalolin rashin tsaron da ta'addar da ke sauya launi da salo.

Dama dai an dora daukacin kasafin ne bisa wani gibin da ya kai kusan kaso 50 cikin dari na kudaden shiga na kasar, gibin kuma da Abujar ke fatan samu daga basukan ciki dama wajen tarrayar Najeriyar.

Karin Bayani: Najeriya: Faduwar darajar Naira na kara kamari

Dr Hamisu Ya'u masanin tattalin arziki ya ce Abujar na bukatar sauyin lissafi a cikin neman ceton kasafin da ke barazanar rushewa.

Ginin Majalisar dattijan Najeriya a Abuja
Ginin Majalisar dattijan Najeriya a AbujaHoto: Uwais Abubakar Idris/DW

Majiyoyi dai sun ce Abujar na tunanin sake Nazari bisa kasafin da yake fatan hakar gangar mai miliyan 1.78 a kusan kullum tare da sayar da ita a kan dala 78.

Duk da cewar masu mulkin Najeriyar na sai da man dala 82 kan kowace ganga a yanzu, yawan man da kasar ke hakowa kullum dai bai wuce ganga miliyan 1.5 ba, a yanzu adadin da ke nufin gibin ganga 270,000 a kusan kullum.

To sai dai kuma duk da hakan a fadar Yusha'u Aliyu da ke sharhi ga tattalin arzikin rikicin da ke gaban mahukuntan bai isa tada jijiyar wuya cikin kasar da ke da arzikin danyen man ba.

Kasafin na bana dai na zaman irin sa na farko ga sabuwar gwamnatin kuma zakaran gwajin dafi na sabuwar tarrayar Najeriyar da babu tallafi a cikinta