1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Kenya ta haramta yada labaran bogi

Zulaiha Abubakar
May 16, 2018

Shugaba Uhuru Kenyatta na kasar Kenya ya rattaba hannu kan dokar haramta yada labaran bogi a fadin kasar cikin wata sanarwa.

https://p.dw.com/p/2xqcN
Kenia Symbolbild Smartphones
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Kafa wannan doka dai ta biyo bayan yawaitar labarai marasa sahihanci da fina-finan batsa da kuma yada ayyukan ta'addanci a kafafen sada zumunta na zamani da ya zama ruwan dare a kasar.

ko da yake wasu daga cikin al'ummar kasar sun bayyana shakku game da dalilan da shugaban kasar ya bayar na amincewa da wannan doka tun da fari, inda suka danganta matakin da yunkurin hana masu adawa da mulkin shugaban kasar ta Kenya, cin moriyar fadin albarkacin baki wanda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar musu.

Tun a farkon wannan shekara ce gwamnatin kasar ta rufe wasu manyan gidajen talabijin uku wadanda suka nuna wani taron motsa Jam'iyya da gungun 'yan adawar kasar suka gudanar.