Kasar Senegal ta lashe gasar AFCON
February 7, 2022Talla
Fitaccen dan wasan gaban kungiyar Liverpool da ke kasar Ingila, Sadio Mané, shi ne ya jefa kwallon karshe a ragar kasar Masar da ta basu nasarar lashe gasar.
Da ma dai masu sharhi kan kwallon kafa a duniya sun yi hasashen cewa ta yiwu kasar Senegal ce za ta yi nasara saboda fitattun 'yan wasa da kwarewarsu a kungiyoyin kasashen turai, kana ake kuma kallon karawar kamar ta mutum biyu ce, wato tsakanin Mohammed Salah na kasar Masar da kuma Sadio Mané dan kasar Senegal da suka kasance 'yan kungiya daya ta Liverpool.
Tuni 'yan kasar Senegal suka fara bukukuwa don murnar nasarar da triumphant Lions suka samu, yayin da shugaba Macky Sall ya baiyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu a Senegal din.