1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kasar Turkiya ta mayar da maratani ga EU

Yusuf BalaDecember 15, 2014

Shugaba Erdogan na Turkiya ya alakanta sumame da aka kai kafafen yada labarai da tsaron kasa. Sannan ya ce bai damu da tasirin da zai yi ba ga shigar kasarsa cikin EU.

https://p.dw.com/p/1E4aE
Erdogan PK mit Papst Franziskus 28.11.2014
Hoto: Reuters/T. Gentile

Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiya ya yi watsi da sukar da Kungiyar kasashen Turai ta EU ta yi bayan farmakin mahukuntan birninn Ankara a kan kafafan yada labarai. Ya bukaci kungiyar ta rike duk wani tsokaci da take son yi a wajenta.

Kungiyar ta EU dai ta yi kakkausar suka kan ayyukan 'yan sanda na dirar mikiya ga wasu kafafen jarida da na talabijin wadanda ke da alaka da wanin shehin addinin Islama Fethullah Gulen da ke zama a Amirka. 'Yan sanda da 'yan jarida masu tsara shirye-shirye na daga cikin mutane 27 wadanda aka tsare bisa zargin shirya wata makarkashi da ka iya kawar da gwamnatin kasar.

Kungiyar ta EU ta ce wannan farmaki na mahukuntan kasar ta Turkiya ka iya zama wani tarnaki ga kokarin da kasar ta dade ta na yi wajen ganin ta shiga kungiyar ta EU.