Zimbabuwe ta dauki alwashin inganta alaka da China
April 3, 2018Talla
Shugaba Mnangagwa ya bayyana haka ne a wannan Talata yayin da yake ganawa da shugaban kasar China Xi Jinping a wata ziyara irinta ta farko da ya kai China, bayan darewarsa kujerar shugabancin Zimbabuwe.
A baya dai tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya kyautata alakar kasashen biyu duk kuwa da cewar an zarge shi da yada cin hanci a lokacin mulkinsa.
Tun a baya China ta cigaba da alaka da Zimbabuwe duk kuwa da janye alaka da kasar da kasashen yammacin Turai suka yi bisa rahotannin keta haddin dan Adam a lokacin mulkin Robert Mugabe.