1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Nijar da Senegal sun dauki hankalin jaridu a Jamus

Mohammad Nasiru Awal MA
March 12, 2021

Dambarwar siyasar Nijar da Senegal, manyan batutuwa ne da hankula suka koma a kansu a baya-bayan nan a yankin yammacin Afirka. Zaben kasa a Nijar dai ya bar baya da kura.

https://p.dw.com/p/3qXWL
Niger Treffen der afrikanischen Union in Niamey - Mahamadou Issoufou
Hoto: AFP/I Sanogo

Za mu fara sharhi da labarun jaridun Jamus kan nahiyarmu ta Afirka da jaridar Süddeutsche Zeitung wadda ta yi tsokaci kan halin da  Jamhuriyar Nijar ke ciki a daidai lokacin da Shugaba Mahamadou Issofou ke shirin yin bankawana da madafun ikon kasar. Ta ce watakila ba a taba samun wata kasa ba wadda lokacin da shugabanta zai bar fadar mulki ke da tarin matsaloli kamar Nijar ba. Jaridar ta ce kasar na a sahun gaba a jerin kasashe da suka fi fama da talauci, a arewacinta musamman a iyakarta da kasar Libiya wani bangare na kungiyar Al-Kaida ke aiki a kudancinta wato a Najeriya Boko Haram ce ke aika-aika sannan daga kasashe makotanta wato Mali da Burkina Faso, kungiyoyin masu ikirarin Jihadi ke mata barazana; ga kuma matsalar bazuwar hamada sakamakon sauyin yanayi, sai kuma bunkasar jama'a.

Sai dai jaridar ta ce shugaban kasa Mahamadou Issoufou na shirin mika ragamar mulki ga zababben shugaban kasa cikin lumana, a wani abin da ke zama irinsa na farko tun bayan samun 'yancin kasar daga Faransa a 1960. Watakila saboda wannan dalilin ne gidauniyar Mo Ibraim ta karramar shugaban mai barin gado. Sai dai ga 'yan adawar Nijar, Shugaba Mahamadou Issoufou, ba cikakken dan dimukuradiyya ba ne, musamman a zaben 2016, an jefa dan adawa mai farin jini a kurkuku.

Senegal Proteste der Opposition
Hoto: Zohra Bensemra/REUTERS

Fushin matasa a kasar Senegal, wannan shi ne taken labarin da jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta buga a tsokacin da ta yi na halin da ake ciki a Senegal. Ta ce karar da aka yi na wani fitaccen dan adawa a Senegal ta janyo gagarumar zanga-zanga mafi girma cikin shekaru, inda a Dakar da wasu biranen kasar dubun dubatan matasa suka fantsama kan tituna. A farkon mako wata kotu ta ba da belin Ousmane Sonko, wanda ya shafe kusan kwanaki hudu a tsare, kafin daga bisani a gabatar da shi a gaban alkali, wanda ya sake shi a kan beli sakamakon zargin da ake yi masa na yi wa wata mata fyade.

Ousmane Sonko wanda ya zo na uku a zaben shugaban kasa, zai iya kalubalantar Macky Sall a zaben shugaban kasa na 2024. Kasar ta Senegal wacce ake yi wa kallon daya daga cikin kasashen Afirka ta Yamma masu bin sahihin tafarki na dimukuradiyya, wacce kuma ta kwashe shekaru da dama cikin kanciyar hankali, a karon farko gwamnati ta baza sojoji kan tituna domin murkushe masu bore. Akalla mutum biyar suka rasu a tashin hankalin da aka yi tsakanin masu boren da jami'an 'yan sanda.

Ita ma jaridar Süddeutsche Zeitung, ta yi sharhi kan boren tana mai cewa Senegal daya ce daga cikin kasashe kalilan masu sahihin tsarin dimukuradiyya a nahiyar Afirka, amma yanzu matasa sun fara juya wa shugaban kasar baya. Ta ce zanga-zangar da ke samun goyon bayan jam'iyyun adawan da wasu kungiyoyi na farar hula ta kasance mafi muni cikin shekaru masu yawa. Kame dan adawa Ousmane Sonko shi ne musabbabin wani boren da ke barazanar gurgunta zaman lafiya da lumana a kasar ta Senegal.