1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kataloniya ta balle daga Spain

Yusuf Bala Nayaya AH
October 2, 2017

Gwamnatin Kataloniya ta yi wani zama na sirri a wannan rana ta Litinin domin daukar mataki na gaba bayan da ta bayyana gagarumar nasara a zaben a ware daga Spain.

https://p.dw.com/p/2l6ym
Spanien Barcelona Referendum über Unabhängigkeit - Protest vor dem Rathaus in Barcelona
Hoto: Reuters/A. Gea

An dai kai ga nuna yatsa tsakanin gwamnatocin na Bercelona da Madrid an kuma gwabza fada tsakanin masu zabe da 'yan sanda inda kimanin mutane 800 suka samu raunika lokacin da masu neman cin gashin kan na yankin na Kataloniya suka fita don kada kuri'a. Shi dai shugaban gwamnatin kasar ta Spain  Mariano Rajoy ya sake jadada cewa maganar kuri'ar raba gardama a yankin na Kataloniya ya sabawa kundin tsarin mulkin kasar.

Spanien Carles Puigdemont in Barcelona
Carles Puigdemont Jagoran masu fafutuka na Kataloniya a tsakiyyaHoto: Reuters/Catalan Goverment/J. Bedmar Pascual

Ya ce: ''Mun yi abin da ya kamata mu yi kamar yadda doka ta tanada a kokari na kare martaba ta demokradiyya kuma za mu yi duk mai yiwuwa wajen kare martabarta ga duk wanda ya so yi ma ta kutse muna gaya masa abin da zai yi ya sabawa dokar kasa, da sunan haramtacciyar kuri'ar raba gardama."

Shugaban yankin na Kataloniya Carles Puigdemont ya bayyana cewar al'ummar yankin sun zabi ficewa daga kasar Spain kuma wannan gibi ne babba ga mahukuntan Madrid sanin irin alfanun da yankin ke da shi.Ya ce kasar Spain sun yi rashi mafi girma na abin da suka rasa a baya al'ummar Kataloniya sun zabi zama masu cin gashin kansu. Puigdemont har ila yau a wannan rana  ya yi zama da 'yan majalisar gwamnatinsa inda suke tunanin mataki na gaba, bayan kuri'ar raba gardamar, yayin da shi ma Mariano Rajoy, shugaban gwamnatin Spain zai gana da shugabannin jam'iyyar Popular Party kafin daga bisani su tsara zama a majalisa kan wannan batu da ya tada hankula a Spain a gwamman shekaru.