Ceto wasu 'yan Nijar daga 'yan bindiga
January 19, 2021Za dai a iya cewa wanna ne karo na farko da mahukuntan jihar ta Katsina suka kubutar da wasu da aka yi garkuwa da su daga Jamhuriyar ta Nijar, kuma tuni gwamnan jihar ta Katsina Aminu Bello Masari ya bayar da umarnin mayar da su garuruwansu a jihar Maradi da ke Jamhuriyar ta Nijar, bayan da aka kai mutanen a fadar gwamnatin jihar bayan an kubutar da su.
Karin Bayani: Dakon mahukunta su ceto yaran da aka sace a Katsina
Sai dai gwamnan ya ce nasarar ci gaba da kubutar da mutanen da suke, ba sulhu ba ne saboda ba zai kara shiga yarjejeniyar sulhu da 'yan bindigar ba.
Masana tsaro a Najeriyar dai kamar Al-ameen Isa na da nasu hangen kan ceto 'yan Jamhuriyar ta Nijar da 'yan bindigar suka sato daga kasarsu tare da yin garkuwa da su.
Karin Bayani: Najeriya: Ana zubar da jini a Arewa
Sannu a hankali dai mahukuntan jihar Katsina na ci gaba da karbo mutanan da 'yan bindigar suka sace domin neman kudin fansa ba tare da biyan ko sisi ba, a cewar mahukunta. Ko a makonni biyun da suka gabata ma, an yi nasarar ceto mutane 104 daga hannun maharan.