1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kayan agaji da likitoci sun isa Port-Sudan

April 30, 2023

Jirgin farko shake da Ton takwas na kayan agaji da kuma jam'an likitotci ya sauka a safiyar wannan Lahadi a Sudan, a daidai lokacin da aka shiga mako na uku da barkewar rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/4Qj74
Jami'an agaji sun yi jigiliar magunguna da likitoci daga Amman zuwa Sudan
Jami'an agaji sun yi jigiliar magunguna da likitoci daga Amman zuwa SudanHoto: ICRC/AFP

Jirgin da ya taso daga birnin Amman ya sauka ne a birnin Port-Sudan da ke gabar ruwa a nisan kilomita 850 da Khartun inda a can ne fadan da ake gwabzawa ya fi tsananta. Kayayin da jirgin ya kawo sun hadar da magunguna da za su ba da damar kula da sama da mutane 1.500 daga cikin 4.599 da aka kididdige sun jikkata tun fara rikicin.  

Wannan kayan agaji dai na isowa ne a daidai lokacin da harkokin ke rincabewa a Sudan inda kungiyar likitoci na gari na kowa ta sanar da dakatar da duk wasu ayyukan jin kai sabili da barin wutar da ake wanda ya kawo katsewar aiki a kusan kashi 80%  na gidajen asibitoci da ke kasar.