Yin gashi da ganyen Kaba
March 11, 2020
Wannan wani shago ne da ake gudanar da sana'ar gyaran gashi cikinsa a Nairobi. Kimanin shekaru biyu ke nan da gwamnatin kasar ta Kenya ta dauki matakan tsabtace mahalli da suka hada da zubar da shara barkatai da kuma amfani da leda a fadin kasar, hakan ya tursasawa wata matashiya yar shekaru 28 a kasar ta Kenya bullowa da wata sabuwar fasaha ta yin amfani da ganyen Kaba wajen yiwa mata karin gashi.
Matashiyar dai na jifar tsuntsu biyu da dutse daya inda ta ke taimakawa wajen kawata gashin kai ga mata sana kuma a hannu guda ta taimaka wajen tsabtace muhalli duba da cewa a can baya a kan yi amfani gashin kanti ne sabanin a yanzu da matashiyar ta kirkiro fasahar yin amfani da kaba ganin cewa ita kaba ana iya kara sarrafa ta zuwa wani abun daban, Assumpta Khasabuli ta kara da cewa.
'' Na kwammace in yi amfani da kaba wajen karin gashi domin ko ruwa ya taba kan mace ba zai yi wari ba, sana kuma yana taimakawa wajen karin tsawon gashi, idan kuma aka kitsa shi baya warwarewa.''
Alfanun mfani da Kaba wajen kawata gashin kai bai tsaya ga tsabtar muhalli ba kawai har da rangwame wanda ya sa a yanzu mata ke yawan amfani da shi. Catherine Okutoi wata mai shagon gyaran gashi ce da kuma take amfani da kabar da Assumpta ke sarrafawa.
'' Gashin na kaba yafi dadin aiki domin kuwa ana iya amfani da shi har sau biyu sabanin na shago da sau daya ne kawai ake iya amfani da shi, banbancin dai kawai shine na kaba kan dauki lokaci wajen kitsa shi amma ya fi tsawo inda shi kuma na kanti yana da saukin aiki.''
Assumpta Khasabuli kan yi tafiyat tsawon kilomitoci 400 zuwa yankin Kakamega da ke yammacin Nairobi babban birnin kasar ta Kenya wurin da take samo ganyayyakin na kaba tare da taimakon ma'aikatanta wanda daga bisani idan ta dawo gida take sarrafa kabar ta hanyar matse ruwan da ke cikinta daga bisani kuma ta shanyata har sai ta bushe. Assumptar dai ta ce tana da burin bunkasa sana'ar tata tana mai cewa.
'' Gwamnatin Kenya ta farga da wannan abin da na kirkiro wanda ya yi daidai da bukatarta na yin awon gaba da duk wani nau'in gashin kanti da aka yi amfani da shi, wannan ya bani kwarin gwuiwar yin tunani bullowa da wanna fasahar.''
Mata da dama ne dai a kasar ta Kenya masu sha'awar ganin sun kayata kashin kansu ke tururuwa zuwa shagunan da ake amfani da gashin na kaba wajen kitso.