An bude rumfunan zaben Kenya
August 9, 2022Talla
An bude rumfunan zaben shugaban kasa a kasar Kenya a safiyar wannan Talata, inda madugun adawa Raila Odinga da ke samun goyon bayan shugaba mai barin gado ke fafatawa da mataimakin shugaban kasa William Ruto da ke tutiya da gwagwarmayarsa da ta kai shi har mukamin mataimakin shugaban kasa.
Karfin mutanen biyu da karbuwarsu a siyasar Kenya ya sanya wasu ke tunanin watakila aje zagaye na biyu a karon farko a tarihin siyasar kasar da ke zama mafi karfin tattalin arziki a gabashin Afirka. Mutum sama da miliyan 22 ne ake sa ran za su kada kuri'a zaben.