'Yan bindiga sun sace wata baturiya a kasar Kenya
November 21, 2018Talla
Matar mai suna Sylvia Constanza Romano, 'yar shekaru 23 da haihuwa ta na aiki ne a karkashin kungiyar Africa Milele Onlus da ke a yankin Kilifi. Wani ganau mai suna Ronald Kazungu Ngala, ya ce a kan idanunsa suka diran ma makarantar suka kuma nemi ya nuna musu inda matar ta ke. Hukumomin Kenya sun ce suna aiki tukuru don ganin an kubuto matar a raye.
Mayakan jihadi na El-Shabab na kasar Somaliya sun yi kaurin suna a sace mutane musanman Turawa daga wannan yankin ko don neman kudin fansa.