An gano gawar mutanen da suka mutu suna azumi
April 23, 2023'Yan sanda a kasar Kenya sun shaida cewa sun tono karin gawarwakin mutum akalla ashirin da daya a ci gaba da binciken da suke kan wata kungiya ta tsafi da mambobinta suka mutu a sakamakon tsananin 'yunwa, bayan sun shafe dogon lokaci suna azumin da jagoransu Makenzie Nthenge ya nemi su yi, domin su samu damar haduwa da Yesu Almasihu. Yara kanana na cikin gawarwakin da masu binciken suka gano a dajin Shakahola da ke Kenyar.
A makon jiya ne aka fara gano gawarwakin wasu mutane hudu da aka ce sun mutu a sakamakon tsananin 'yunwa daga azumin da suke yi, bisa tilastawar jagoransu Makenzie, ba ya ga wasu da aka tarar da sauran numfashi da suka kanjame a dajin, saboda azumin da suke yi. Yanzu dai an kama Mista Makenzei tare da wasu mukarrabansa domin gurfanar da su a gaban kotu.