Kenya: An tsare alkali bisa zargin cin hanci
August 28, 2018Tsare alkali Philomena Mwilu ya zo shekara guda bayan da wasu jerin masu shari'a ciki har da ita suka soke zaben shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta a watan Agusta 2017, hukuncin da ya sa aka sake shirya zabe na biyu a watan Oktoba wanda 'yan adawa suka kaurace masa.
A lokacin da yake yi wa manema labaru bayanai, darektan da ke kula da gabatar da kara, Noordin Haji, ya ce yana da shaidun da ke nuna cewa alkali Mwilu ta yi amfani da mukaminta wajen azirta kanta tare da kin biyan haraji. S ai dai an saki Philomena Mwilu bayan da ta biya beli na kudin shillings miliyan 5 (kudin Euro 42,000).
Tuni da bayyana aniyar kalubalantar wannan zargi da ake yi mata saboda ta saba wa doka. a kwanakin baya ne Shugaba Kenyatta ya kaddamar da yaki da cin hanci da rashawa bisa raunin tattalin arzikin da wannan kasa ta gabashin Afirka ta fada sakamakon almubazzaranci daga manyan jami'an gwamnati.