Kenya: Binciken rantsar da Raila Odinga
January 31, 2018Talla
A jiya Talata ne dai, Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban jama'a a birnin Nairobi a bainar dubban magoya bayansa, bisa ikirarin gwamnatin Uhuru Kenyatta haramtacciya ce.
Sanarwar gwamnati na bayyana matakin na jiya, a matsayin yunkurin kifar da zababbiyyar gwammatin Janhuriyar Kenya. Gabannin bukin rantsar da Odinga dai, babban Alkalin Kenyan ya yi gargadin cewar, wannan yunkuri tamkar cin amanar kasa ce.
Ya zuwa yau Laraba dai wasu gidajen talabijin masu zaman kansu na cigaba da zama a rufe, matakin da gwamnati ta ce na bangaren binciken da take gudanarwa dangane da yayata rantsar da madugun 'yan adawar.