1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya da Afirka ta Kudu a jaridun Jamus

Abdullahi Tanko Bala MAB
July 21, 2023

Tsadar rayuwa da ta haddasa zanga-zanga a Kenya da hikimar da Afirka ta kudu ta yi amfani da ita wajen sa shugaban Rasha Vladimir Putin kaurace wa taron Brics na daga cikin baututuwan da suka dauki hankalin jaridun Jamus

https://p.dw.com/p/4UELk
Masu zanga-zanga da 'yan sanda sun yi fito na fito a Kisumu na KenyaHoto: James Keyi/REUTERS

Jaridar die Tageszeitung ta yi shrhinta ne a kan zanga-zangar gama gari da 'yan adawa suka kira a kasar Kenya kan tsadar rayuwa da karin haraji. Duk da cewa 'yan sanda sun haramta duk wani gangami, amma zanga-zangar ta gudana da farko cikin lumana kafin daga baya ta rikide zuwa tarzoma. Gwamnatin ta dauki matakai na rufe makarantu a manyan birane uku na kasar da suka hada da Nairobi da kuma Kisumu domin kare dalibai daga fadawa cikin hadari

Tsadar rayuwa ta addabi 'yan kenya

Kenia protest gegen die Regierung in Nairobi
Matasan Nairibi sun fusata sakamakon matsalar tsadar rayuwaHoto: John Muchucha/REUTERS

Dalilin zanga-zangar dai shi ne jan hankalin gwamnati ga tsadar makamashi da kuma tashin gwauron zabi na farashin kayan abinci. Sai dai arangama tsakanin 'yan zanga-zangar da suka rika jifa da duwatsu da kuma 'yan sanda da suka rika harba hayaki mai sa hawaye ta jawo mutuwar mutum guda da kuma jikkata wasu da dama. Kungiyoyin kare hakkin dan Adam sun gargadi gwamnati kan amfani da karfi fiye da kima a kan masu zanga zangar.

Jaridar ta die tageszeitung ta tunato cewa tun lokaci annobar Corona aka rika samun karin farashin mai a kasashen Afirka da dama. Sai dai bayan kawo karshen annobar ta Corona, gwamnatoci da dama sun ci gaba da kara haraji domin samun damar biyan dumbin bashin da ke kansu. Alkaluman Bankin Duniya sun nuna bashin da ke kan kasar Kenya ya kai kashi 67% na daukacin abin da kasar ke samu a shekara, wanda ya sa makudan kudaden da ta kashewa wajen biyan bashi ya fi abin da take kashewa a fannin tsaro da Ilmi da lafiya.

Putin ya yada kwallo kan taron Brics

Russland Wladimir Putin
Shugaba Putin na Rasha ya fasa halartar taron Brics a Afirka ta KuduHoto: ALEXEY BABUSHKIN/SPUTNIK/AFP

A bisa yarjejeniya ta fahimtar juna, shugaban Rasha ba zai halarci taron kolin kungiyar kasashen BRICS a Afirka ta Kudu ba. Wannan shi ne sharhin jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, inda ta ce Afirka ta kudu ta yi nasarar amfani da hikima wajen shawo kan shugaban Rasha Vladimir Putin don kaucewa rikicin diflomasiyya. Tsawon watanni hudu lauyoyi da jakadu suka shafe suna auna nauyin da aka dora wa gwamnatin ta Afirka ta Kudu kan yadda za ta kama shugaba Vladimir Putin idan ya halarci taron BRICS na shugabannin kasashen Brazil da Rasha da India da kuma Afirka ta Kudu a watan Augusta.

Ofishin shugaban Afirka ta Kudu ya sanar da cewa shugaban Rasha bisa yarjejeniya ta fahimtar juna ya amince ba zai halarci taron ba, a maimakon haka zai tura ministan harkokin waje Sergei Lavraov wanda zai wakilce shi. 

Ramaphosa ya fita halin tsaka mai wuya

Afrikanische Delegation zu Besuch in Russland
Shugaba Ramaphosa da takwaransa Putin na Rasha sun saba haduwa a tarukaHoto: AP

Kwana guda bayan wannan ne shugaban Afirka ta Kudun Cyril Ramaphosa ya fidda sanarwa inda ya bayyana cewa kama Putin tamkar kaddamar da yaki ne kamar yadda Rasha ta yi ikrari, Ramaphosa ya ce yin hakan ya saba da kundin tsarin mulkin kasarsa na zama sila ta fadawa hadarin yaki da Rasha. A saboda haka ya ce gwamnati ta bi hanyoyi na doka don samun maslaha da kuma kauce wa bata dangantaka da Rasha. A baya dai an yi ta rade-radin za a mayar da taron zuwa Chaina. Wannan dambarwa ta jefa gwamnatin Afirka ta kudu cikin halin tsaka mai wuya a cikin gida inda Jam'iyyar adawa ta Democratic Alliance ta nufi kotu domin samun sammaci game da kamen.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung ta ce ga kasar Afika ta Kudu dai, wannan kokari ne na kare kanta daga tozarta a idanun duniya. A shekarar 2015 ma dai, an samu makamancin wannan yanayi inda kotun shari'ar manyan laifuka ta  duniya ICC ta bukaci hukumomin Afirka ta Kudu su kama tsohon shugaban Sudan Omar al Bashir idan ya ziyarci kasar. Sai dai gwamnatin ba ta yi hakan ba, matakin da kotun kolin kasar ta ce gwamnatin ta aikata ba daidai ba.