SiyasaAfirka
Kenya da Amurka na son a rage wa Afirka nauyin basuka
May 23, 2024Talla
Yayin ziyarar kwanaki uku ta aiki da shugaban Kenya William Ruto ke yi a Amurka ne dai ya zanta da Shugaba Joe Biden a game da wannan bukata.
Wannan shi ne karo na farko cikin sama da shekaru 15 da ake samun wani shugaba na Afirka ke ziyara makamancin wannan a hukumance a birnin Washington.
Shugabannin biyu sun kuma ce suna shirye nan ba da jimawa ba, da su bayyana wata sabuwar taswiarar samar da ci gaba tsakanin kasashen Kenya da Amurka da suka yi wa lakabi da Nairobi-Washington Vision.
Tuni ma dai Amurka ta bayyana ware dala miliyan 250 da za a yi amfani da su wajen taimaka wa kasashe matalauta dake fama da radadin tattalin arziki.