Rushewar gini a Kenya ya halaka dalibai
September 23, 2019Talla
Tuni dai hukumomin kasar da suka tabbatar da afkuwar wannan ibtila'i ta bakin da kakakin fadar gwamnati Cyrus Oguna. Rahotanni sun nunar da cewa an dauki yaran da suka jikkata zuwa babban asibiti na Kenyatta National Hospital a kan babura, kasancewar jami'an agaji ba su iso wajen ba sai bayan sa'a guda da rabi. Dalibai biyu cikin wadanda ke kwance a asibitin dai na cikin mawuyacin hali.