SiyasaAfirka
Dan sandan Kenya ya bindige mutane a kan titi
December 7, 2021Talla
Rundunar 'yan sandan kasar Kenya ba ta kai ga fitar da wata sanarwa kan lamarin ba. Sai dai rahotanni sun ce dan sandan ya fara harbe matarsa ne, inda daga baya kuma ya juya kan mutanen da suka zo wucewa su ma ya bude musu wuta.
Kamfanin dillancin labaran Jamus na DPA ya ce lamarin ya haifar da zanga-zanga daga wasu matasa da suka fara kona tayoyi suna kira da lallai sai an biya su diyyar mutanen da ake zargin dan sanda ya halaka.