Kenya: Kudurin doka na shirin haifar da rudani
June 13, 2024Talla
Ana sa ran ministan kudin Kenyar ya gabatar da wani kudurin dokar kudi mai cike da cece-kuce, wanda ya kushi sabbi da kuma karin kudaden haraji. Majalisar dokokin kasar ta amince da tsarin kashe kudin, sai dai kuma kudurin dokar da aka samar da nufi cike gibin karancin kudi a asusun gwamnati ka iya haifar da rudani.
'Yan siyasa da 'yan kasa da kuma kungiyoyin 'yan kasuwa na sukar wannan kudurin na gwamnati, wanda ta ce dole ne ta samar saboda rage yawanbashin da take ciyo wa.
Masana sun yi gargadin cewa, kudurin zai kara jefa rayukan jama'a cikin matsi, wanda a irin haka ne; a bara aka gudanar da jerin zanga-zanga wadanda suka bar baya da kura.