1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya: Odinga ya rantsar da kansa

Ramatu Garba Baba
January 30, 2018

Madugun adawa da ya sha kayi a babban zabe Raila Odinga ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasar Kenya na al'umma a wannan Talata a gaban dubban magoya bayansa da suka yi dafifi don halartar bikin.

https://p.dw.com/p/2rlad
Kenia "Vereidigung" von Raila Odinga in Uhuru Park in Nairobi
Hoto: picture-alliance/AP Photo/B. Curtis

Odinga ya dauki matakin rantsar da kansa ne duk kuwa da gargadi daga ma'aikatar shari'a da ke baiyana matakin a matsayin laifi na cin amanar kasa da ka iya tada zaune tsaye a kasar da ta yi kaurin suna wajen barkewar rikice-rikice na bayan zabe.

Dubban magoya bayan Odinga sun yi dafifi a wani dandali da ke a Nairobi babban birnin kasar. Magoya bayan jagoran sun baiyana farin cikinsu da ganin wannan rana.

Kawo yanzu bai fadi daga inda ya samo sakamakon da ya ba shi tabbacin lashe zaben ba, ya zuwa wannan lokacin da ya sha rantsuwar kama aikin.