1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenya ta haramta sayar da mayukan sauya launin fata

Zulaiha Abubakar MA
February 26, 2019

https://p.dw.com/p/3E79I
Nigeria Hautbleichungsmittel
Hoto: Getty Images/AFP/S. Heunis

Masu sayar da sinadaran sauya launin fata a kasar Kenya sun yi Allah wadai game da yadda gwamnatin kasar ta haramta kasuwancin mai da sabulun canza launin fata wanda galibi mata ke amfani da su. 

Hukumar kula da ingancin kaya a Kenya ta tabbabtar da cewar mafiya yawan mai da sabulan da mata a kasar ke amfani da su don haskaka fatarsu, na dauke da sinadaran da ke matukar cutar da lafiya kamar sinadarinHydroquinone da Mercury.

Allunan talla a Kasar ta Kenya na dauke da hotunan mata masu hasken fata like da irin wadanan mayuka da sabulai. Tuni aka zargi fitattun mata da mawaka kamar Vera Sidika  da cusa wa mata wannan akida ta shafe-shafe.

Hukumar lafiya ta Duniya ta danganta cutar hanta da lalacewar jijiyoyi da haihuwar jarirai marasa ingantacciyar lafiya da wannan dabi'a ta shafe-shafe don canjin launin fata.