Kenya na shirin harba tauraron dan Adam
April 3, 2023Talla
Kenya za ta harba tauraron ne tare da SpaceX kamfanin Amrikan kamar yadda ma'aikatar tsaron Kenya da hukumar kula da sararin samaniya ta kasar suka sanar. Tauraron dan Adam,din da ake kira da sunan Taifa-1 Nation-1 a cikin harshen Swahili, wani gungun masana ne masu bincike na Kenya suka samar da shi. zai dai rika samar da sahihan bayanai da za su amfani bangaren noma da samar da abinci da, sarrafa albarkatun kasa da bala'o'i da sa ido kan muhalli. Kasar Kenya da ke da karfin tattalin arziki a gabashin Afrika, ta fuskanci fari mafi muni a shekarun baya-baya nan, bayan da aka kwashe tsawon lokaci ana samun damina marasa kyau.