Kenya: Namun daji sun mamaye garuruwa
June 3, 2022Talla
'Yan sanda sun bude wuta kan masu zanga-zangar a garin Masimba mai tazarar kilomita 170 a kudu maso gabashin Nairobi babban birnin kasar. Wadanda suka fusata da mutuwar wani malamin makarantar da giwa ta kashe.Sun kona tayoyi tare da rufe hanyar da ta hada Nairobi da Mombasa mai tashar jiragen ruwa.