Kenya zata dauki likitoci aiki daga waje
May 14, 2018Talla
A shekara ta 2017 ne dai shugaba Uhuru Kenyata ya amince da kudurin, sai dai an fara cimma yarjejeniyar shirin ce a yayin ziyarar da ya kai Kuba a watan Maris da ta gabata.
Kungiyar likitocin kasar Kenya dai ta koka kan yadda gwamnati ke kokarin haramta wa 'yan kasar damar samun aiki, kungiyar ta ce akwai likitoci 2,000 da ke jiran a daukesu aiki.
Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce kowani likita daya a kasar Kenya na kula da marasa lafiya dubu 16,000 a maimakon likita daya ga majinyata 1000 kacal, sai dai gwamnatin ta zargi likitocin da rashin kwarewar aiki.