1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kenyatta ya kama ragamar mulki a karo na biyu

Usman Shehu Usman
November 28, 2017

Uhuru Kenyatta ya sha rantsuwar sabon wa'adin shugabancin kasar Kenya, bayan kace-nace da ya biyo bayan zabe na biyu da 'yan adawa suka kauracewa shiga.

https://p.dw.com/p/2oOae
Kenia Amtseinführung Präsident Kenyatta
Hoto: Reuters/T. Mukoya

Bukin da aka yi a babban filin kwallon kafan birnin Nairobi ya cika makil, inda har aka yi ta turereniya wajen shiga. Wasu daga 'yan kasar ta Kenya dai sun bayyana ra'ayinsu kan ranzuwar da shugaban Nasu ya yi a yau.

"Rantuwar a wurina wani abun al'ajabi ne, domin mun dade muna jiran wannan ranar, har muka fara jin kamar akwai wata matsala da ke faruwa ga kasarmu. Yanzu muna cikin murna. Na san kuma kowa ma na cikin nishadi. Muna cikin murna, mun kuma karbi wannan labarin da hannu bibbiyu"

"Yau ina cikin farin ciki, mun zo ranar da shugaban kasarmu. Muna addua'ar hakan ya kawo karshen  tashin hankalin kasarmu, zaman lafiya ya dawo. Kowa ya koma harkarsa kamar da, ma'aikata su koma wuraren aiki. Muna murna kan hakan"

Kenia Oppositionsführer Raila Odinga
Hoto: Getty Images/AFP/Y. Chiba

Sai dai yayin da wannan ke faru a kewayen filin kwallon kafa da aka gudanar da bukin, a wasu anguwannin birnin Nairobi, jami'antsoro sun yi ta dauki ba dadi da 'yan bangan bangaren adawa, inda matasa suka yi ta jifan jami'an tsaro da duwatsu yayin da su kuma suka yi cillawa matasa hayaki mai sahawaye..

Tuni ma dai shi kansa madugun 'yan adawan kasar ta Kenya, ya hallarci wani gangamin 'yan adawa, inda magoya bayansa suka ci gaba da kai ruwa rana da jami'an tsaro, abinda ya kaiga hatta tawagar Odinga ta sha hayaki mai sa hawaye. Odinga ya sanar da cewa shi ma za'a rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, a ranar 12 ga watan Disemba mai zuwa, abin da ke nuni da cewa akwai alamar ci gaban tashin hankali a kasar Kenya.

Kenia Unterstützer bei der Amtseinführung von Kenyatta
Hoto: Getty Images/AFP/S. Maina

Shi dai sabon shugaban kasar Kenya mai shekaru 55 Uhuru Kenyatta, a jawabinsa ya yi ikirarin daukar matakin hada kan kasar kenya, kana ya ce daga yau an soke takardun bisa ga duk dan asalin kasasr Afirka da ke son zuwa Kenya, wanda ya bude babin hadin kai a kasashen Afirka.