1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kerry: Masalahar kasa biyu na cikin rudani

December 28, 2016

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya gargadin Isra'ila ta guji yin gaban kai a masalahar rikicinta da Falasdinawa

https://p.dw.com/p/2Uysz
USA Außenminister John Kerry zu Lage in Nahost
Hoto: Getty Images/Z. Gibson

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry a wani gagarumin jawabi da ya yi kan zaman lafiya a gabas ta tsakiya, ya yi gargadin cewa batun fadada matsugunai na gwamnatin Isra'ila a gabar yamma yana jefa shirin zaman lafiya tsakaninta da Falasdinawa cikin mawuyacin hali. 

Kerry yace babu wani mai tunanin zaman lafiya da zai yi watsi da wannan barazana da shirin fadada matsugunan ke haifarwa. Kerry ya kara da cewa batun ya wuce na fadada matsguna kawaii, yana mai cewa alamu sun nuna Isra'ila na wani gagarumin shiri na kwace yankin gabar yamma da kuma hana Falasdinawa raya yankinsu

Yace masalahar kafa kasashe biyu da za su zauna daura da juna ita ce kadai hanyar da za'a tabbatar da adalci da zaman lafiya mai dorewa tsakanin Israila da Falasdinawa. Ita ce kuma kadai hanyar da za'a tabbatar da makomar Isra'ila a matsayin kasar Yadudawa kuma kasa mai bin tafarkin dimokradiyya.